China Ta Ware Dala Miliyan Dubu 60 Don Bunkasa Kasashen Afirka

[ad_1]

A wajen babban taron koli na (FOCAC) da ake gudanarwa tsakanin shugabanin kasashen Afirka da China karo na 7, shugaba Xi Jinpin ya bayyana cewa akwai bashi da tallafi na musamman na dalar Amurka Miliyan dubu 60, da kasarsa ta ware don bunkasa fannoni daban-daban na rayuwa da kuma inganta manyan aiyuka a kasashen Afirka.

Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, na daga cikin tawagar shugaba Muhammadu Buhari. Wanda kuma ya ce Najeriya na daga cikin manyan kasashen Afirka da zasu bukaci kudi dayawa daga cikin kudin da aka ware.

Da yake yiwa Sashen Hausa na Muryar Amurka ‘karin haske kan yadda Najeriya za ta ci moriyar kudaden da aka ware, gwamna Badaru, ya ce aikin gina tashar wutar lantarki a tsaunin Mambila, da ayyukan gina layin dogo da ake shirin yi a fadin kasar, da kuma aikin sake farfado da titunan da suka lalace, duk na daga cikin manyan ayyukan da Najeriya za ta nemi tallafi aiwatar da su.

Cikin kudaden da kasar China da ‘yan kasuwarta suka ware don tallafawa kasashen Afirka, akwai dala milyan dubu 15 da zasu kasance tallafi na musamman da kuma basussukan da basu da kudin ruwa, akwai kuma dala milyan dubu 20 da za a bada bashi domin tsara manya-manyan ayyuka a kasashen Afirka.

Taron dai zai baiwa manyan ‘yan kasuwar China karfin gwiwa su saka hannun jari na akalla dala Miliyan dubu 10 domin bunkasa saka hannun jari da cinikayya tsakanin kasashen Afirka da kasar China.

A lokacin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ke jawabi wajen taron, ya ce gwamnatinsa ta samu tallafi da gudunmawa da basussuka daban-daban da ya haura dala Miliyan dubu biyar, wanda gwamnatin ta yi amfani da su wajen yin manya-manyan ayyuka na ‘kasa, kamar layin dogo da gina manyan hanyoyi da kuma sha’anin noma, wandan suka kawo sauki da gina rayuwa ga al’ummar Najeriya.

Domin karin bayani saurari hirar gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru da Sahabo Imam Aliyu.

[ad_2]

More News

Ƴan sanda sun kama masu sayen kuri’a a zaben gwamnan Edo

Jami'an rundunar Æ´an sandan Najeriya sun kama wasu mutane 9 da ake zarginsu da sayen kuri'a da kuma mallakar kuri'ar da aka riga aka...

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...