Chelsea ta koma ta uku a teburin Premier League

Olivier Giroud scores for Chelsea against Crystal Palace

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Giroud ne ya fara ci wa Chelsea kwallo kuma na uku kenan da ya zura a raga tun da aka ci gaba da wasannin Premier League

Chelsea ta doke Crystal Palace da ci 3-2 a wasan mako na 34 a gasar Premier League da suka fafata ranar Talata a Selhust Park ta kuma koma ta uku a teburi.

Chelsea ce ta fara cin kwallo a minti na shida da fara wasa ta hannun Olivier Giroud, sannan Christian Pulisic ya kara na biyu.

Daga nan Palace ta zare kwallo daya ta hannun Wilfried Zaha, kuma haka suka je hutu Chelsea ta ci biyu ita kuwa Palace da daya a raga.

Bayan da aka ci gaba da karawar zagaye na biyu ne Chelsea ta kara na uku ta hannun Tammy Abraham wanda ya shiga karawar daga baya.

Sai dai minti daya tsakani da Chelsea ta ci kwallo na uku ne, Christian Benteke ya zare daya.

Nasarar da Chelsea ta yi ya sa ta koma ta uku a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakaninta da Leicester City wacce ta koma ta hudu.

Leicester za ta ziyarci Arsenal a daya wasan mako na 34 da za su kece raini a gasar ta cin kofin Premier League wacce tuni Liverpool ta cinye kofin bana.

Crystal Palace mai maki 42 tana ta 14 a kasan teburin shekarar nan, kuma ta yi rashin nasara a wasa hudu a jere.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...