Champions League: Real Madrid na tsaka mai wuya a wasa tsakaninta da Man City

Getty

Bayanan hoto,
Real Madrid ce kungiya daya tilo da ta taba lashe gasar gasar zakarun Turai 13

Idan ana maganar gasar Champions ce a Turai, idan Real Madrid ta É—aga hannu babu wata kungiya da ta isa ta lankwasa mata.

Amma idan ana maganar wasa tsakaninta da Man City, za a iya cewa da karfin gwiwa City za ta fito, idan aka yi la’akari da wasanni ukun da aka buga a baya-bayan nan, biyu duka an yi canjaras ne daya kunnen doki, da kuma wanda aka yi kurman diro.

Sai wasan farko da aka yi a na siri daya kwale na Champions din wannan shekarar gabanin annobar korona, wanda Real Madrid ta sha kashi a hannun City da 2-1.

Matsalolin da Real Madrid ke fuskanta

Matsalar farko an doke Madrid 1-2 har gida, wanda kuma ita ta fara cin kwallo kafin daga baya a farke a kara mata.

Yanzu kuma za ta je Ingila gidan Manchester City kuma har sai ta ci kwallo biyu babu ko daya ko uku da daya kafin ta iya cin ye City.

Sergio Ramos ba zai buga wasan ba saboda katin da aka ba shi a wasan da aka buga na farko a Santiago.

Real Madrid ta rage kwarjini tun bayan tafiyar Cristiano Ronaldo zuwa Juventus.

Yawan wasannin da Manchester City ta yi nasara a cikinsu a Champions wani abu ne da ake ganin zai iya yiwa Real Madrid mummunan tasiri.

Duk da cewa ta lashen gasar La Liga amma wasannin karshe na gasar sun nuna a irin yadda Madrid ba ta iya zira kwallaye ma su yawa kamar a baya.

Mafi yawan ‘yan wasan Madrid sun fara gajiya saboda yawan buga wasanni kamar su Benzema da Modric da Kroos da dai sauransu.

Sai dai Bale wanda ke da alaka mai tsami tsakaninsa da mai horas da kungiyar Zinedine Zidane watakila ba zai buga wasan ba.

Amma ana yiwa Zinedine Zidane kallon mai nasara a wannan gasa don haka wasu na ganin ba za a iya hasashen mai zai faru ba har sai an buga wasan.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...