Champions League: Ansu Fati ya kafa tarihi a Barcelona

Ansu Fati

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tun bayan fara wasa a LaLiga ta bana, Fati ya ci kwallo biyu tare da taimakawa wajen cin wata daban

Matashin dan wasa Ansu Fati ya kafa tarihi a kungiyar Barcelona ta Sifaniya bayan ya buga wasan da Barca din ta sha da kyar a hannun Borussia Dortmund a Talatar farko ta Champions League na 2019/2020.

Dan shekara 16 da kwana 351, Fati ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya buga wa Barcelona wasa a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Kafin wannan lokaci dai dan wasa Bojan Krkic ne ke rike da kambun, inda ya buga wasa tsakanin Barcelona da Lyon a shekarar 2007 yana dan shekara 17 da kwana 22.

Celestine Babayaro na Najeriya shi ne ke rike da kambun baki daya a gasar ta Champions League. Ya fara buga wasa a kulab din Anderlecht yana dan shekara 16 da wata biyu.

Tun bayan fara wasa a LaLiga ta bana, Fati ya ci kwallo biyu tare da taimakawa wajen cin wata daban.

  • Jan-aikin da ke gaban Liverpool na kare Champions League
  • Chelsea: Matashin dan wasa Mason Mount zai yi jinya

An haifi Ansu Fati a ranar 30 ga Oktoban 2002 a kasar Guinea-Bissau da ke yankin Afirka ta Yamma.

Ya zauna tsawon wata shida a kasar kafin daga bisani ya koma garin Herrera a kudancin Sifaniya bayan mahaifinsa mai suna Bori ya samu aikin tukin mota a fadar magajin garin.

Mahaifinsa ya ce dan wasan ya koma Barcelona ne bayan Albert Puig, daraktan kungiyar ta matasa, ya mika tayin daukarsa.

Bori ya shaida wa gidan rediyon RAC1 cewa bayan daraktan ya kawo masu ziyara har gida, Barcelona ta ba su wurin zama a cikin farfajiyar hedikwatar kungiyar ta matasa.

Saboda haka ne suka koma birnin Barcelona baki daya da zama.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...