Ce-ce-kuce ya kaure kan maye gurbin alkaliyar kotun Amurka da ta mutu

Ruth Bader Ginsburg

Bayanan hoto,
Ruth Bader Ginsburg

Alkaliyar alkalan kotun koli ta Amurka Ruth Bader Ginsburg ta mutu tana da shekaru tamanin da bakwai.

Ta kwashe tsawon lokaci tana fama da cutar kansa.

Tuni aka fara muhawa kan ko shugaba Trump na da damar maye gurbinta gabanin zaben kasar da za a yi a watan Nuwamba.

Bayanai sun ce tuni wasu rahotannin bayan fage daga fadar White House ke cewa shugaba Trump zai yi farat daya wajen maye gurbinta kafin zabe da kuma rantsar da duk wanda ya samu nasara a zaben watan Nuwamba.

Shi dai abokin hamayyarsa na jam’iyyarsa Democrat Joe Biden, ya kalubalanci damar da shugaban yake da ita ta maye gurbin alkaliyar.

An yi kasa ka da tutoci a birnin Washington don girmama marigayiyar jim kadan bayan sanar da da mutuwarta,

Jama’a sun taru a wajen kotun koli don bayyana jimaminsu, yayin da suke daga tutocin Amurka da kyandiran aci bal bal suna rera sunanta cikin wake.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...