Ce-ce-ku-cen Kayyade Adadin Haihuwa a Najeriya

A Najeriya, ana ta ka-ce-na-ce dangane da wasu kalamai da aka danganta da Ministar kudi Zainab Ahmed inda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito cewa ta ce kasar na duba wani tsari da zai kayyade adadin yaran da mace za ta haifa.

Rahotanni sun bayyana cewa Ahmed ta bayyana hakan ne yayin wani taro da ke dubi kan farfado da tattalin arzikin kasar da aka yi a Abuja.

Sai dai Ministar ta musanta rahotanni inda ta ce ba haka take nufi ba.

“Gwamnatin tayarraya tana tuntubar shugabannin gargajiya da na addinai, kan yadda za a bai wa jama’a shawara kan amfani da tsarin ba da tazarar iyali.” Ministar ta ce a shafinta na Twitter.

Ta kara da cewa “sam ba mu ce za mu kayyade adadin haihuwa ba. Mene ne tazarar iyali?, wannan wani tsari ne na ba da tazara tsakanin yaran da za a haifa.”

Kafin ta musanta rahotannin, shafukan yanar gizon wasu jaridun kasar sun ruwaito Ministar tana cewa hukumomin Najeriya na kokarin samar da wani tsari da zai kayyade adadin yaran da mace za ta haifa a kasar.

Sun kuma ruwaito tana cewa daya daga cikin manyan kalubalen da shirin farfado da tattalin arzikin kasar ke fuskanta shi ne yawan al’umar kasar.

Adadin al’umar Najeriya a yanzu kamar yadda kiyasi ke nunawa ya haura miliyan 190.

Wata kididdiga da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, ta nuna cewa yawan al’umar kasar zai haura miliyan 300 nan da shekarar 2050.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...