CBN ya yi barazanar daukar mataki kan bankunan da ke boye takardun naira

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargadi Bankunan Ajiya na Kudi kan boye kudi da karkatarwa, yana mai cewa irin wannan aiki za iya jawo hukunci mai tsanani.

A wata sanarwa da ta fito ranar 13 ga Nuwamba, 2024, wacce Daraktan Riko na Sashen Kula da Kudi, Muhammad J. Olayemi, ya sanya wa hannu, kuma CBN ya fitar a ranar Juma’a, bankin ya bayyana matakan tabbatar da rarraba kudi yadda ya kamata.

CBN ya tunatar da bankunan kan gudanar da binciken sirri da na ba-zata don dakile yin abin da ya saba wa doka da naira da kuma tabbatar da ingantattun hanyoyin rarraba takardun naira, musamman yayin da bukukuwan karshen shekara ke karatowa.

More from this stream

Recomended