CBN ya sauya fasalin kudin naira 1000 500 da 200

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da sanarwar sauya fasalin sabbin kudin Naira, 1000 500 da kuma 200.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele shi ne ya bayyana haka cikin wata ganawa da yayi da manem labarai a ranar Laraba.

Emefiele ya ce sabbin kudin za su fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Disamba 15 2022.

A yayin da za a cigaba da amfani da tsofaffin takardun kudin har ya zuwa ranar 31 ga watan Janairu na shekarar 2023.

Ya kuma shawarci yan Najeriya da su rika kai kudin su bankuna domin a canza a basu sabon kudin da aka sauyawa fasali.

Gwamnan na CBN ya ce dalilin daukan matakin shi ne sun lura cewa da yawa daga cikin kudaden da ake da su basa cikin bankuna a ajiye face suna ajiye a hannun mutane.

More from this stream

Recomended