Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna ta tabbatar wa Gwamna Uba Sani cewa za ta ci gaba da yi masa addu’o’i tare da goyon baya domin tabbatar da ingantaccen jagoranci a jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata wasika da shugaban kungiyar na jihar, Rev. (Dr) Caleb Maáji Bawa, ya sanya wa hannu ranar 18 ga watan Agusta, 2025.
Kungiyar ta kuma tabbatar da aniyar ci gaba da hadin kai da gwamnatin jihar Kaduna “wajen inganta hadin kai.”
A cewar wasikar, gwamnan ya cancanci yabo saboda kokarin da yake yi wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar.
Kungiyar ta kuma gode wa gwamnan bisa amincewa da gyaran hanyoyi da dama da suka hada da PAN Drive-Television Garage-Sabo road, Samrada-Romi-Karatudu-Gonin Gora road da kuma Nasarawa-UNTL-Zenith Bank road.
CAN Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Tallafawa Gwamna Uba Sani Da Addu’o’i
