Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da naɗin, Daniel Bwala a matsayin mai taimaka masa na musamman kan sadarwa da kuma kafafen yaɗa labarai.
Bayo Onanuga mai bawa shugaban ƙasa shawara na musamman kan watsa labarai da tsare-tsare ne ya sanar da haka a cikin wata wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Tsohon mataimaki na musamman ga, Alhaji Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023 Bwala ya yi aiki tuƙuru wajen ganin Atiku ya yi nasara a zaɓen.
Amma kuma bayan kammala zaɓen ne ya lallaɓa ya dawo ɓangaren Tinubu abun da ya haifar da ce-ce-kuce.