Chelsea ta lallasa Burnley inda ta ci ƙwallo huɗu cikin kusan minti 23 a karawar farko bayan Roman Abramovich ya sanar da sayar da ƙungiyar.
Tun kafin wasan Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya bayyana cewa matakin attaijirin na Rasha rudani ne, amma kuma ƴan wasansa sun yi rawar gani.
Kai Havertz, ne ya ci ƙwallo biyu bayan Reece James ya ci ƙwallo ta farko da kuma ƙwallo ta ƙarshe da Cristian Pulisic ya jefa a ragar Burnley.
Sakamakon bai yi wa Burnley daɗi ba domin za ta ci gaba da zama a ƙasan teburin Premier.
Bayan yaƙin da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine ne, Abramovich ya fito ya sanar da cewa yana neman mai sayen Chelsea saboda zargin yana da alaƙa da Putin, amma magoya bayan ƙungiyar sun ta yayata sunansa a filin wasa.
An ware minti ɗaya kafin wasan domin nuna goyon baya ga Ukraine.

