Buhari yafi kaso 80 na mutanen Najeriya,koshin lafiya -Ngige

[ad_1]








Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chriss Ngige ya ce shugaban kasa, Muhammad Buhari ya fi kaso 80 na mutanen kasarnan koshin lafiya.

Ngige ya bayyana haka a matsayin martani kan damuwar da wasu suke nunawa akan shekarun shugaban kasar da kuma lafiyarsa dama yadda zai shafi gudanar da ayyukansa.

Da yake magana da yan jaridu a Awka babban birnin jihar Anambra, Ngige ya ce a matsayinsa na likita zai iya cika baki kan lafiyar jikin shugaban da kuma ta ƙwaƙwalwarsa.

Ministan ya kwatanta Najeriya da kasar Malaysia, ya ce lokacin da kasar dake yankin Asia ta shiga cikin rudanin siyasa dana tattalin arziki ta dogara kan Mahathir bin Mahmud domin ya jagorance ta

“Wannan mutumin (Buhari) ya na cikin koshin lafiya fiye da kaso 80 na yan Najeriya.”

“Ni likita ne, zan iya fada maka cewa lafiyayye ne fiye da mutanen da suke ganin batun lafiyarsa abun damuwa ne.”




[ad_2]

More News

Ƴan sanda sun kama masu sayen kuri’a a zaben gwamnan Edo

Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya sun kama wasu mutane 9 da ake zarginsu da sayen kuri'a da kuma mallakar kuri'ar da aka riga aka...

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...