Daya daga masu neman takarar gwamna daga jihar Cross Rivers John Upan Odey, ya ce ba a bashi damar ya zabi ko da kansa ba ma, domin ko kayan zaben ma bai gani ba, “ita dai wannan jam’iyya ta shugaba Buhari ya kamata a ce ta na aiki bisa kare ka’ida da hakkin dukkan ‘yan jam’iyya amma mu kam an nuna ma na durmukel inda a ka sanar da sunan wani ba tare da yin zaben ba.”
Shi ma wani dan takarar Edem Duke, ya ce ta yaya za su yi ta kuka a daji tamkar ba su da ‘yan uwa kuma ba a saurare su ba kan korafin da su ka mikawa uwar jam’iyya na neman a soke zaben fidda gwanin.
Korafin dai ya kai ma har ga gwamnonin kan su kamar Nasiru Elrufai na Kaduna da ya gana da shugaba Buhari kan tikiti ba hamaiya na takarar Majalisar Dattawa da jam’iyya ta ba wa Sanata Shehu wanda ba sa danyen ganye.
Ko ma dai me za a ce shugabannin APC sun ce shugaba Buhari zai lashe zaben 2019.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa Sanata Lawwali Shu’aibu ya ma yi gugar zana ga babbar jam’iyyar adawa ta PDP “duk ‘yan takarar su in ka dora su kan sikeli, Buhari zai yi rinjaye a kan su”
Ba mamaki bayan kammala mika sunayen ‘yan takarar jam’iyyu a hukumar zabe, a samu kofar musanya wasu ‘yan takarar don samun maslaha daga matakin jam’iyya.