Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar Kofi Annan

[ad_1]

Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana jajensa bisa mutuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Mr Kofi Annan.

Mr Annan ya rasu ne ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiyar, in ji wata sanarwa da Gidauniyar the Kofi Annan Foundation ta fitar.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya fitar, ya ambato Shugaba Buhari yana mika ta’aziyyarsa ga shugaba da al’umar kasar Ghana – mahaifar Mr Annan.

A cewar sanarwar, “Shugaba Buhari, wanda ya kira shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ta wayar tarho daga London, ya mika alhinin ‘yan Najeriya da kasashen ECOWAS member, ganin irin muhimmancin marigayin a harkokin kasashen duniya da kuma hangen nesansa na sauya Yammacin Afirka da ma nahiyar baki daya.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa marigayi Mr Annan mutum ne mai dattako da kaunar jama’a da kankan da kai, abubuwan da suka sanya shi yin zarra a duniya

Shugaban nan Najeriya ya kuma jinjinawa marigayi Mr Annan musamman a kokarin da ya yi na yaki da HIV/Aids a Afirka da kuma kaddamar da Muradun ci gaban Karni.

Ya yi addu’ar Allah ya bai wa iyalai da ‘yan uwansa hakurin rashinsa.



[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...