Buhari ya yi ta’aziyya kan likita 20 da korona ta kashe

A

Shugaban Najeriyar ya ce kyautata jin daɗi ma’aikatan lafiya da ke kan gaba a yaƙi da annobar, wani muhimman abu ne da gwamnatinsa ke bai wa fifiko.

Buhari ya bayyana haka ne a cikin wani saƙon ta’aziyya da ya aika wa Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya game da likitocin da annobar korona ta kashe a ƙasar.

Saƙon wanda kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya wallafa, bai yi ƙarin bayani ba a kan lokacin da likitocin 20 suka mutu, da kuma ko sun mutu ne a karo daban-daban ko kuma lokacin guda.

Jimillar mutum 82,747 ne suka harbu da cutar korona zuwa ranar Asabar a Najeriya, kuma annobar ta yi ajalin maras lafiya 1,246.

Shugaba Buhari ya ce mutuwar musamman ma’aikatan lafiyan ƙasar da ke kan gaba a yaƙi da cutar korona, abin takaici ne saboda irin waɗannan ƙwararru suna sanya rayukansu cikin kasada don kuɓutar da sauran al’umma.

“Ma’aikatan lafiyanmu na yin sadaukarwa mafi girma ga ƙasa, bisa tanadin aikinsu na jin ƙai, kuma gwamnatin nan za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin ta biya buƙatunsu,” in ji Buhari.

Ya nunar cewa ma’aikatan lafiyan na aiki ne cikin matsanancin tarnaƙi, amma kuma ana raina gudunmawarsu ta ceton rayuka.

Shugaba Buhari ya ce kuma ba tare da wata fargabar furta kalamai masu cin karo da juna ba, babu wani lada da ya kai sadaukarwar da ma’aikatan lafiyan ƙasar ke yi, kuma gwamnatinsa za ta bai wa fannin kyautata jin daɗinsu fifikon da ya kamace shi.

More from this stream

Recomended