Buhari ya samu gudunmuwar motocin kamfen 100

Yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari ya samu gudunmawa bayan samun kyautar motoci 100 da kuma ginin ofishin kamfen da wani jigo a jam’iyar APC ta jihar Niger ya bayar .

Gudunmawar motocin da kuma ginin mai hawa uku ta fito ne daga, Muhammad Musa wanda akafi sani da Sani 313 dantakarar kujerar sanatan mazabar Niger ta gabas a karkashin jam’iyar APC.

Bikin bayar da gudunmawar wani ɓangare ne da aka shirya shugaban kasa Muhammad Buhari zai yi yayin yakin neman zabensa da ya kai jihar amma aka dage saboda rashin isasshen lokaci.

Gwamna Abubakar Sani Bello shine ya bude ginin tare da karbar motocin a madadin shugaban kasa.

Bello ya godewa jigon jam’iyar da ya bayar da gudunmawar kana ya shawarci kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Buhari ta BSO da kuma kwamitin yakin neman zaben shugabansa da suyi amfani da kayan da aka bayar gudunmawar yadda yakamata.

More from this stream

Recomended