Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno.

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa da ta faɗawa birnin Maiduguri sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alou dake wajen birnin.

Wani saƙo da tsohon mai magana da yawun shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya fitar ya ce Buhari ya yi jinkirin kai ziyarar jajen ne saboda lokacin da ambaliyar ta tafi hutu a ƙasar waje.

Tsohon shugaban ya sauka a filin jirgin saman Maiduguri inda ya samu tarba daga gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum da kuma Sanata Ali Ndume.

Buhari ya yabawa gwamnatin jihar da kuma ta tarayyya kan yadda suka haɗa kai wajen tallafawa mutanen da abun ya shafa.

Ya ƙara da cewa duk da cewa ya turo wakilai domin su jajanta al’ummar jihar a lokacin da abun ya faru yana ƙasar waje duk da haka bai gamsu ba sai da yaji akwai buƙatar da yazo ganewa idonsa sannan ya jajantawa jama’a.

Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum da kuma Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garba Alamin Elkanemi  sun godewa tsohon shugaban ƙasar kan ziyarar da ya kawo.

More from this stream

Recomended