
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki ta kwanaki 8 a kasar Saudiyya inda kuma yayi aikin Umarah.
Buhari ya baro Saudiyya ta filin jirgin saman Sarki Abdulaziz dake Jeddah a ranar Laraba.
A cewar kamfanin Dilllancin Labarai na Najeriya NAN, jami’an gwamnatin Saudiyya, shugabannin addini da kuma wasu manyan jami’an ofishin jakadancin Najeriya a can na daga cikin waɗanda suka yi shugaban bankwana.