Buhari ya ce zai daure barayi da dama

[ad_1]

Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa kasar daga hutu shi ne daure barayi.

Shugaban ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talbijin na NTA jim kadan bayan ya isa fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban birnin kasar.

Da aka tambaye shi game da abin da zai sa a gaba bayan ya yi hutun kwana goma, Shugaba Buhari ya ce “za mu daure barayi da dama wadanda suka jefa mu cikin matsin tattalin arziki. Da ma na san ana sa ran zan yi hakan, kuma zan yi.”

Yaki da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da Shugaba Buhari ya yi alkawarin aiwatarwa lokacin da yake yakin neman zabe.

Gwamnatin Shugaban na Najeriya ta gurfanar da manyan jami’an tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan a gaban kuliya, inda ake zarginsu da sace kudaden gwamnati.

Sai dai jam’iyyun hamayya da wasu masu sharhi na zargin Shugaba Buhari da daure ‘yan adawa kawai.

A cewar su, yawancin jami’an gwamnatinsa da ‘yan jam’iyyar APC mai mulki na da hannu a zarge-zargen cin hanci amma ba a dauki matakin hukunta su ba.

‘Yan kasar da dama na son Shugaba Buhari ya daure duk mutumin da aka samu da hannu wajen taba lalitar gwamnati ba tare da sani ko sabo ba.

Shugaban na Najeriya ya ayyana sha’awarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019, kuma masu sharhi na ganin kalaman nasa ka iya yin tasiri wurin sake zabensa.

[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...