
Hakkin mallakar hoto
Presidency
Shugaba Buhari ya ce jazaman ne sai an bullo da manufofin da za su bunkasa sarrafa kayan Afirka idan ana so yarjejeniyar ta yi nasara
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci maras shinge a Afirka yayin babban taron kungiyar Tarayyar Afirka cikin makon gobe a Nijar.
Da farko dai kasar ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar wadda ta fara aiki a karshen watan Mayu, sai dai yanzu ta ce za ta yi hakan bayan zuzzurfar tuntubar da ta yi a cikin gida.
A sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter Fadar shugaban kasar da maraicen ranar Talata, ta ce za ta yi hakan ne domin cin moriyar tattaunawar da ake yi da nufin samun kariyar da ta wajaba ga matsalolin fasa-kwauri da kuma jibge wa kasashen Afirka shara.
Najeriya, mafi girman tattalin arziki a nahiyar, na cikin kasashe kalilan da ba su rattaba hannu kan yarjejeniyar ciniki maras shinge ta Afirka ba.
Amma shawarar shiga tsarin wannan gamayya a yanzu zai yi matukar karfafa gwiwar masu burin ganin wannan yarjejeniya ta tabbata.
Manufar yarjejeniyar ita ce kawar da haraje-haraje tsakanin kasashen nahiyar tare da kafa wata kasuwa wadda mutum biliyan daya da miliyan 200 ke ci.
Haka kuma za ta taimaka wajen juya jimillar sama da dala tirliyan 2.2 na kayan da ake sarrafawa a nahiyar.
Bayanai sun ce ban da Najeriya, kasashen Eritriya da Benin su ma sun zabi janye jiki daga yarjejeniyar.
A baya, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan barin makwabtan kasashe su je su cika Nijeriya makil da kayayyaki masu rangwamen farashi, da kuma lalata kokarin karfafa gwiwar farfado da masana’antun kasar da suka durkushe har ma bunkasa noma.
Sai dai kwamitin da gwamnatin ta kafa don tantance tasirin shiga gamayyar ya ba da shawara a makon jiya cewa kamata ya yi Najeriya ta yi tunanin shiga.
Sanarwar fadar shugaban Nijeriya ta ambato Muhammadu Buhari na cewa domin samun nasarar yarjejeniyar ciniki maras shinge ta Afirka, jazaman ne sai sun bullo da manufofin da za su bunkasa sarrafa kayan Afirka.
Don haka Afirka ba kawai manufar ciniki take bukata ba, har ma da wani tsarin sarrafa kaya a masana’atun nahiyar.
Ya kara da cewa matsayinsu a sauk’ak’e yake, suna goyon bayan kasuwanci maras shinge matukar za a yi shi cikin adalci kuma a aiwatar da shi bisa doron raba daidai.