Buhari ne dan takarar APC a 2019

Shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo

Jam’iyyar APC mai mulki a Nigeria ta sake tsaida shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar ta a zaben shekara mai zuwa, da za a yi a watan junairu.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan da ministar mata Aisha Jummai Alhassan ta sanar da yin murabus tare da ficewa daga jam’iyyar APC.

Ita ce ta biyu cikin ministocin gwamnatin shugaba Buhari da ta fice daga jam’iyyar da barin aiki a watannan.

Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar APC mai mulki a matakin jihohi, inda aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin wasu gwamnoni da mataimakansu.

Misali rikici tsakanin gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari da mataimakinsa Malam Ibrahim Wakkala bayan gwamnan ya tsaida dan takarar da ya ke son ya gaje shi.

An kara samun wasu ‘yan takara da ake kira G8 duk dai a Zamfarar da suma suka samu matsalar da ta janyo suka dare gida biyu.

Wasu dai na ganin zaben fitar da gwani da aka dauki salon wakilai, zai iya kawo son rai saboda zargin wakilan su na zaban wanda gwamna ke so ya gaje shi.

Ya yin da wasu ke ganin zaben kato bayan kato shi ya cancanta, dan al’uma su zabi abin da suke so ba wani ya zaba musu ba.

A makwannin da suka gabata yawancin ‘ya’yan jam’iyya mai mulki sun yi ta ficewa zuwa jam’iyyar adawa wato PDP.

Kawo yanzu jam’iyyar PDP ba ta fidda wanda za ta tsayar dan takarar shugaban kasa ba, da zai kalubalanci shugaba Buhari.

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...