BH sun kashe jami’an Civil Defence 4 a Kaduna

Hukumar tsaro ta Civil Defense ta tabbatar da mutuwar jami’anta huɗu a wani harin kwanton ɓauna da ƴan bindiga suka kai musu  a yankin Farin-Ƙasa dake ƙaramar hukumar Chukun ta jihar Kaduna.

A ranar 18 ta watan Nuwamba ma hukumar ta fitar da wata sanarwa dake cewa wasu da take zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai harin kwanton ɓauna kan jami’an hukumar dake aikin sanya idanu a jihar Kaduna inda aka kashe jami’an hukumar su 7.

Afolabi Babawale, mai magana da yawun hukumar ta NSCDC ya ce lamarin ya faru ne lokacin da tawagar jami’an suke duba turakun babban layin wutar lantarki dake Shiroro a jihar Niger.

A wata sanarwa ranar Juma’a, Afolabi ya ce an gano gawarwaki huɗu daga  cikin jami’an su 7 da wanda aka bayyana sun ɓace da farko.

Ya ce jami’ai biyu sun dawo da rauni a yayin da guda ɗaya kuma har yanzu ba a san inda yake ba.

Ya ce shugaban hukumar, Ahmed Audi ya jajantawa ma’aikatan hukumar kan faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended