Boko Haram ta kashe mutane da dama a Borno

Soja

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Rahotannin daga Arewa maso gabashin Najeriya suna cewa ce ‘yan Boko Haram sun kashe a kalla mutane 12 yayin da suka kai hari a kauyuka biyu a Jihar Borno.

Harin da aka kai a ranar Laraba da daddare ya sa wasu sun ji ciwo yayin da gidaje da dama suka kone.

Rudunar sojin Najeriya ta ce ta kori maharan, amma ba ta bayyana adadin wadanda suka mutu ba a harin ko kuma suka ji rauni ba.

‘Yan sintiri sun shaida wa BBC cewar mayakan sun far wa kauyen Kalari da kuma Amarwa mai makwabtaka, suna masu neman abinci.

Maharan sun harbe wadanda suka yi kokarin tare su.

  • Sojojin Nigeria sun sake kwace garin Gudumbali daga Boko Haram
  • Boko Haram ta kai wa sojojin Najeriya hari

Yawancin mazauna garin sun tsere zuwa cikin daji yayin da ‘yan bindigar suka shiga gidajensu kuma suka kona su.

Kakakin rundunar sojin Najeriya a Maiduguri Kanal Onyema Nwachukwu ya ce dakarun Bataliya ta 222 sun dakile kokarin harin kuma an tura sojojin sama domin neman maharan.

Dukkan kauyukan biyu- Kalari da Amarwa sunakarkashin Konduga ne, wata gunduma a jihar Borno wadda ta sha wahalar hare-haren Boko Haram.

A watan Disambar bara, mutane shida ne aka kashe a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wata kasuwa a Amarwa.

An kara kashe wasu mutum 10 a watan Afrilu lokacin da ‘yan mata biyu suka kai harin kunar bakin wake a kauyen.

A farkon wannan makon, wasu mayaka sun kashe wata ma’aikaciyar lafiya ta Red Cross da aka sace tare da abokan aikinta biyu, a wani harin da aka kai wata shida da ya gabata.

A wata sabuwa, rahotanni sun ce wani sojin Najeriya ya kashe kansa bayan harbe wani abokin aikinsa tare da harbin wasu hudu a jihar ta Borno.

Sai dai kuma rundunar sojin Najeriyar ta ce harbi ba bisa niyya ba ne ya janyo mutuwar sojojin biyu.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...