Ƴan bindiga sun sako mutane 56 da suka yi garkuwa da su jihar Niger

Yan bindiga sun sako sauran manoma 56 da suka yi garkuwa da su daga kauyen Adunu dake kusa da kauyukan dake karamar hukumar Paikoro ta jihar Niger bayan sun shafe watanni 6 a hannunsu.

Mazauna garin sun ce an sace mutanen ne a ranar 14 ga watan Maris inda suka cigaba da zama a hannun yan bindigar bayan da iyalansu suka gaza biyan kudin fansa a kan lokaci.

Tun da farko yan bindigar sun saki wani fefan bidiyo inda suka yi barazanar kashe ragowar mutane da suke rike da su matukar ba a biya kudin fansa ba.

Jami’in tsare-tsare na kungiyar Justice, Development and Peace Commission, Rabaran Bahago Dauda Musa ya ce ba a jima da sako mutanen ba.

More from this stream

Recomended