Binciken Magu: Ina makomar yaƙi da cin hancin Najeriya?

TWITTER/EFCCOFFICIAL

Hakkin mallakar hoto
TWITTER/EFCCOFFICIAL

Image caption

Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu

Wasu masharhanta a Najeriya na da ra’ayin cewa matuƙar zarge-zargen da ake yi wa muƙaddashin shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, suka tabbata, to duk nasarorin da gwamnati ke cewa ta samu, za su tashi a tutar babu.

Suka ce ƙurar da ta turnuƙe shugabancin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawar ta Najeriya na iya kai wa ga sallamar Ibrahim Magu, ko a sauya masa wurin aiki, ko ma a gurfanar da shi gaban kotu.

Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata na kungiyar CAJA, mai rajin tabbatar da shugabanci na gari, ya ce matuƙar aka samu Magu da lam’a ko aibu cikin al’amuransa to duk nasarorin da gwamnati ke iƙirari za su samu tawaya.

“Domin sallah daga liman take ɓaci, in har Magu da lam’a cikin al’amuransa, to dukan abubuwan da ake iƙirari, sun tabbata cewa ba a yi nasara ba,” in ji mai rajin tabbatar da shugabanci na gari.

Labarai masu alaka

Dakata ya ƙara da cewa: ”Idan a karshe, an tabbatar da zarge-zarge kan Magu, to ka ga dole sai ya fuskanci shari’a, a masa hukunci daidai da abin da ya aikata, shi ma kuma idan ta kama ya dawo da abubuwan da ake zargin ya wawura”.

A cewarsa, kwamitin na iya zama na uku da ya jefa alamar tambaya a kan nagartar Magu, domin a baya hukumar tsaron farin kaya ta ba da rahoton yana da kashi a gindi lokacin da aka bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da shi.

Ya ce kuma wannan ya nuna matsalar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, domin sau da yawa mutane ake yaƙa bisa ga umarnin wasu maimakon mayar da hankali kan yaƙi da rashawa bil haƙƙi da gaskiya.

“Shi ya sa za ka ga duk wanda ya zo, aka gama amfani da shi wajen musgunawa ‘yan siyasa da waɗanda ba a so, shi ma sai su yi watsi da shi,” in ji Kwamared Dakata.

Image caption

Tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribado

Daga kafa hukumar EFCC zuwa yanzu dai ta yi shugabanni hudu, kuma babu daya daga ciki da za a iya cewa ya yi rabuwar arziki da hukumar.

Alal misali shugaban hukumar na farko Malam Nuhu Ribado, an daura masa mukamin mataimakin babban sipetan `yan sanda sannan aka nada shi shugabanta, amma a karshe aka yi masa kora da hali ta hanyar tura shi kwas na rana tsaka, daga nan ya yi bankwana da kujerar.

Haka ita ma Farida Waziri, wadda ta gaje shi, haka aka raba ta da mukamin ba girma ba arziki. Duk da cewa gwamnatin wancan lokacin ta ce dalilan cire ta na sirri ne, Farida Wazirin ta yi zargin cewa gwamnati ce ba ta ji dadin yadda take yaki da masu aringizon tallafin mai ba.

Shi ma Ibrahim Lamurde, wato magajin Farida Waziri wata rabuwa ya yi ba tare da sallama ba, kasancewar an tura shi kwas irin na BuhuRibado a daidai lokacin da majalisar dattawan Najeriyar take nemansa domin ya yi bayani a kan wani kudin da hukumar ta kwato, da ake zargin ya salwanta.

Yanzu kuma ga Ibrahim Magu, wanda kamar yadda masu lura da al`umar ke cewa ya kama hanya, saboda ba a taba sauka daga kujerar an sake haye ta ba.

Masu fafutukar yaki da cin hancin dai na ganin cewa wannan dambarwa da ake yi a kan Ibrahim Magu ya jefa gwamnatin Najeriyar a tsaka mai wuya, ko da kwamitin bincike ya same da laifi ko akasin haka, kamar yadda Kabiru Dakata ke cewa:

Zangin cin hanci da rashawa da laifuka na cuwa-cuwa ya raba manyan jami`an gwamnati a da mukaminsu a Najeriya, ciki har da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawan, tsohuwar ministar kudi, Kemi Adeosun, amma batun Ibrahim Magu ya ja hankali ne saboda ana tsammanin wuta a makera ne sai aka samu a masaka kamar yadda ake zargi, ganin cewa ya jagoranci hukumar da ba ta san wani aiki ba face yaki da cin hanci da rashawa.

More from this stream

Recomended