Dalibai a birnin Kano ranar Talata wadanda akasari na jami’ar Yusuf Maitama Sule ne sun fito zanga-zanga a birnin don neman sakin ‘yar Najeriyar nan da ke tsare, Zainab Aliyu.
Hukumomi a Najeriya sun ce Zainab ba ta da laifi domin wasu ne suka saka mata kwayar a wata jaka kuma suka makala sunanta a jiki.
Masu zanga-zangar sun je har gaban karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke jihar Kano.