Bene Ya Rufta Da Mutane A Abuja

[ad_1]
A yammacin yau Juma’a ne wani bene mai hawa biyar ya rufta a yankin Jabi da ke babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da benen ya rufa, ana kan aiki a cikin sa.

Kimanin mutane hudu aka garzaya da su asibiti yayin da jami’an hukumar bayarda agajin gaggawa ke ci gaba da aikin ceto wadanda abun ya ritsa da su.

Jami’an na yunkurin kwashe baraguzan ginin domin ceto mutanen da ginin ya danne.

Wasu rahotannin sun nuna cewa cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da mata.

Izuwa lokacin da aka wallafa wannan labari, ba a san adadin mutanen da wannan abu ya ritsa da su ba.

Haka zalika ba a san musabbin zubewar ginin ba.

Birnin Tarayya dai na fuskantar ruwan sama kusan kowacce rana, wanda ko a yayin da jami’an agajin ke yunkurin ceto mutanen, ruwan sama ake ta tafkawa.
[ad_2]

More News

Ƴansandan sun yi artabu da ƴanbindiga a Abuja

Jami’an ‘yan sanda daga babban birnin tarayya Abuja sun kashe wani dan bindiga tare da cafke uku a wani samame da suka kai.Ƴan sandan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan...

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...