Bello Turji Ya Saki Mutane 32, Ya Yi Alkawarin Daina Kai Hari a Zamfara

Fitaccen malamin addini, Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah, ya bayyana cewa shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji, ya saki mutane 32 da ya yi garkuwa da su tare da bayyana aniyarsa ta dakatar da hare-hare kan manoma a Zamfara. Wannan ya biyo bayan tattaunawa da wasu malamai a cikin dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi.

A cewar Yusuf, sun gana da Turji, Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila. Jita-jitar cewa an kashe Dan Bakkolo karya ce. Wadannan mutanen su ne ke haddasa matsalolin tsaro a yankin, kuma duk sun amince da shirin zaman lafiya.

Ya ce Turji da mukarrabansa sun mika wasu daga cikin makaman da suke amfani da su a matakai daban-daban. Haka kuma, sun bar manoma su koma gonakinsu da ke cikin daji.

A cewarsa, cikin wadanda aka saki akwai mata da yara, kuma sun shafe kusan watanni hudu a hannun masu garkuwa. Wata mace ta haihu a cikin daji, yayin da wata kuma maciji ya sare ta.

Yusuf ya ce yankin Shinkafi na fama da matsalar tsaro ya samu sauki tun bayan shigar malamai cikin al’amuran. Ya kara da cewa suna ci gaba da tattaunawa da Turji, amma ba su bukaci ya mika duka makamansa ba domin kada hakan ya jawo masa barazana daga wasu kungiyoyi da ba su cikin yarjejeniyar.

Ya gargadi malamai da ke suka ko zagin Turji a kafafen sada zumunta da su daina, domin hakan na iya lalata nasarorin da ake samu.

Malamin ya yaba da kokarin Shugaba Bola Tinubu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal da Sanata Shehu Buba wajen daukar matakin zaman lafiya maimakon amfani da karfi kawai.

More from this stream

Recomended