
Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, EFCC ta ce ta kama naira miliyan 32 da dubu 400 da take zargin za a yi amfani da su wajen sayen kuri’a a zaben ranar Asabar a Lagos.
Hukumar ta sanar da haka ne a wani bayani da ta sanya a shafinta na Facebook da cewa jami’anta a jihar ne suka yi nasarar kama kudin.
Bayanin ya nuna cewa mutumin da ake zargi da safarar kudin na hannunta inda ake ci gaba da yi masa tambayoyi.
Hukumar ta EFCC ta kama wadannan kudaden ne ‘yan sa’o’i bayan da rundunar ‘yan sandan Najeriyar a jihar Ribas, ta kudu maso kudanci kasar ta sanar da kama wani dan majalisar wakilan kasar mai ci da ke takarar sake komawa kujerarsa a jam’iyyar PDP da kusan dala dubu 500.
Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa daman ya umarci dukkanin jami’an hukumar da aka sa aikin zabe su mayar da hankali tare da dagewa wajen zakulo duk wani shiri na kumbiya-kumbiya a zaben.
Sannan ya hore su da kada su sassauta wa duk wasu mutane da za su yi yunkurin almundahana a zaben ta hanyar bayar da kudi ga masu zabe ko jami’ai.
Hukumar ta yaki da masu yi wa kasar zagon-kasa ta fannin tattalin arziki ta tura kwararrun ma’aikatanta a kan harkar zaben a dukkanin jihohin kasar da kuma babban birni, Abuja.
EFCC ta sanya lambobin waya a shafukanta na sada zumunta da muhawara domin jama’a su gaggauta sanar da jami’anta a duk inda suka ga ana yin wani abu da ya danganci rabon kudi na almundahana a kan zaben.
Ana ganin wannan kamen kudin da hukumar ta yi a Lagos ya nuna nasarar matakin da ta dauka na kokarin dakile ko kuma rage amfani da kudi wajen sayen kuria a zabukan na Najeriya na 2023.
A ranar Asabar 25 ga watan nan na Fabarairun ne za a yi zaben shugaban kasa da na ‘ yan majalisar dokokin kasar.
Sai kuma ranar 11 ga watan Maris inda za a yi zaben gwamnoni da kuma na ‘yan majalisar dokokin jiha.