Shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPC ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan matsin da suka sake tsintar kansu sakamakon karancin man fetur.
Shugaban kamfanin man, Mele Kolo Kyari ya tabbatar wa BBC cewa ana sa ran matsalar ta yanke cikin ƴan kwanaki kaɗan masu zuwa.
Kalaman Mele Kyari a tattaunawar sa da BBC, na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma a Najeriya ke ci gaba da fuskantar dogayen layukan mai, musamman a manyan biranen ƙasar.
Matsalar ta man fetur, wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tun a shekarar da ta gabata, na ci gaba da jefa al’ummar Najeriya cikin garari, yayin da babban zaɓen ƙasar ke ƙaratowa.
Sai dai Mele Kyari ya ce cikin kwanaki biyu masu zuwa za a samu sauki ko da wahalar bata kare ba baki ɗaya domin hukumomi sun ɗauki matakan da suka dace domin ganin an shawo kan matsalar.
Me ya sa aka gagara shawo kan matsalar?
Malam Mele Kyari ya shaida cewa, dama duk lokacin da aka samu tangarɗa wajen raba fetur ana shiga cikin irin wannan yanayi, kuma a kan ɗau tsawon lokaci kafin a warware.
Mele ya ce suna da tarin mai jibge a kasa wanda za a iya shafe kwanaki 30 ba tare da an wahala ba.
Sai dai tangarɗan da aka samu wanda ya kai ga mutane sun shiga gidan mai suna sayen mai fiye da bukatarsa, shi ke haifar da dogayen layuka.
Sannan ya ce akwai matsaloli kamar ta dauko man daga manyan jirage da ke kan ruwa zuwa defo-defo, kana a kai su gidajen mai.
Sai dai canje-canjen farashi a kasuwar duniya ya shafi wasu ayyukansu.
Mele ya ce wannan ne dalili ya sa idan ‘yan kasuwa sun dauko man ba zai yiwuwa ba, su zo su sayar da shi a yadda gwamnati ta kayyade, wannan shi ne dalilin wahalar feturin.
‘Wasu gidajen mai na nuna haɗama’
Shugaban NNPC ya kuma sake fito da wani batun na yadda wasu gidajen man ke nuna haɗama da tsawala farashin fetur da yawa, yana mai cewa hukumomin da alhakin daidaita farashi ke kan su na bibbiyar lamarin domin shawo kan matsalar.
Malam Mele ya ce sun dau matakan ganin fetur ya wadatu a kasuwa ta hanyar zama da ‘yan kasuwa da abin ya shafa domin tabbatar da cewa man na isa ga manyan biranen Najeriya.
Sannan a wasu wuraren kamar Abuja ana haɗawa da jami’an tsaro domin ganin man ya wadatu ba tare da an boye ba.
Shugaban ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri tare da alkawarta cewa nan bada jimawa ba komai zai daidaita, sauki sai samu a sassan kasar.