BBC Hausa: Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka daga 31 Janairu zuwa 6 Fabrairu

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a sassan Afirka a wannan makon.

Dan Najeriya Oyindamola Kolawole, mai shekara 26, ya na wasan kwalmada jiki a wajen wasannin kwalmada jikin da aka yi a birnin Lagos a ranar Asabar....

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Dan Najeriya Oyindamola Kolawole, mai shekara 26, yana wasan kwalmada jiki a wajen wasannin kwalmada jikin da aka yi a birnin Legas a ranar Asabar….

Ifeoma Amazobi, 22 da abokiyarta na wasan kwalmada jiki a wasan da aka yi a Lagos da ke Najeriya a ranar 1 ga watan Fabrairun, 2020

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wadannan matan biyu na nuna kwazonsu a wajen wasan kwalmada jiki……

Ifeoma Amazobi 'yar shekara 22, na daya daga cikin wadanda suka shirya wasan kwalmada jiki da aka yi Lagos a ranar 1 ga watan Fabrairun 2020

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ifeoma Amazobi ‘yar shekara 22, na daya daga cikin wadanda suka shirya wasan kwalmada jiki da aka yi Lagos a ranar 1 ga watan Fabrairun 2020

Magoya bayan jam'iyyar adawa a Malawi na murna a ranar 4 ga watan Fabrairun 2020.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A babban birnin Malawi Lilongwe a ranar Talata, magoya bayan jam’iyyar adawa sun yi wasanni kala-kala bayan wata kotu ta yi watsi da nasarar Shugaba Peter Mutharika……..

Mata na cashewa a ci gaba da murnar soke nasarar shugaban Malawi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mata na cashewa a ci gaba da murnar soke nasarar shugaban Malawi

A ranar Jumma'a 31 ga watan Janairun 2020, wani yaro a Libya na wasa babur inda ya daga shi a wani wajen shakatawa da ke Tripoli.... 31 January 2020

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A ranar Jumma’a, wani yaro a Libya na wasa da babur inda ya daga shi a wani wajen shakatawa da ke Tripoli….

Wadannan yaran sun dauke hoton nan a ranar Talata ind asuke buga kwallo a Tripoli a ranar 3 ga watan February 2020

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wadannan yaran sun dauke hoton nan a ranar Talata inda suke buga kwallo a Tripoli

A ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu 2020, wani dan yawon bude idanu na wasa a sararin samaniya a Masar a ranar Asabar

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani dan yawon bude idanu na wasa a sararin samaniya a Masar a ranar Asabar

Wani deela na kaya na kirga kudi a bayyanar jama'a a wajen 'yan canjin da ke Mogadishu na kasar Somalia a ranar 5 ga watan Fabrairun 2020.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani dila na kaya na kirga kudi a bayyanar jama’a a wajen ‘yan canjin da ke Mogadishu na kasar Somaliya.

Wata mata da danta sun isa wani asibiti domin neman magani a wani asibiti da ke unguwarsu a Harare na kasar Zimbabwe a ranar 4 ga watan Fabrairu, 2020.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A babban birnin kasar Zimbabwe wato Harare, wata mata da danta sun je wani asibiti mai duhu domin neman magani.

Wasu sojoji na maci a babban birnin Afirka ta Kudu Pretoria gabanin isowar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ta kai ziyara da nufin bunkasa cinikayyar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu a ranar 6 ga watan Fabrairun 2020

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wasu sojoji na maci a babban birnin Afirka ta Kudu, Pretoria, gabanin isowar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ta kai ziyara da nufin bunkasa cinikayyar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu

Wani dan kasar Kenya na karanta jarida mai dauke da hoton tsohon shugaban kasar da ya mutu a ranar Talata Daniel arap Moi a ranar 4 ga wtaan Fabrairu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za mu karkare da hoton yadda wani dan kasar Kenya ke karanta jarida mai dauke da hoton tsohon shugaban kasar da ya mutu a ranar Talata Daniel arap Moi.

Hotuna daga AFP, EPA, PA da Reuters

More from this stream

Recomended