
Ademola Adeleke gwamnan jihar Osun ya yi watsi da batun dake cewa akwai yiyuwar ya fice daga jam’iyar PDP.
Gwamnan ya ayyana biyayyarsa ga jam’iyar PDP a lokacin wani taro na musamman da aka gudanar da shugabannin jam’iyar a ranar Alhamis da daddare.
Adeleke ya ce jita-jitar sauya shekarsa labarai ne na karya.
“Mutanena, dattawan jam’iya da kuma shugabanni ina ayyanawa a gabanku yau cewa bazan koma jam’iyar APC ba ko kuma wata jam’iya,” ya ce.
” Ina nan a PDP kuyi watsi da labaran karya,”
Kalaman na gwamnan na zuwa ne dai-dai lokacin da wasu jiga-jigan yan siyasa ke ficewa daga jam’iyar ta PDP.