Bayyana tsiraici ba uzuri ne na yi wa mata fyaɗe ba – Sheikh Pantami

FMoCDENIGERIA

Hakkin mallakar hoto
FMoCDENIGERIA

Image caption

Sheikh Isa Pantami ya kuma bayyana damuwa kan yadda shari’o’in masu fyaɗe kan shafe tsawon lokaci a gaban kotuna.

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci kuma minista a Najeriya, ya ce babban abin tsoro ne, ƙaruwar saɓon Allah kamar aikata fyaɗe a daidai lokacin da duniya take fama da annoba.

Dr. Isa Ali Pantami ya ce matsalar ƙaruwar fyaɗe baya-bayan nan a sassan ƙasar, “annoba ce ta shigo cikinmu kuma jarrabawa ce, bala’i ne kuma”.

“Abin da ke ba ni tsoro, lokacin da ya dace mu ƙara ƙasƙantar da kanmu, mu koma zuwa ga Allah (SWT)” in ji malamin amma ayyukan laifi suna ƙara yawa. “Bil haƙiƙa, wannan bala’i ne”.

Sheikh Pantami ya bayyana haka yayin wata zantawa da wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza.

Ya ce ba hujja ba ce mutum ya auka wa mace don kawai ta sanya tufafin da yake jin suna fito da tsiraici. “Addini ya wajabta maka, ka runtse ganinka,” in ji Panatami.

A cewarsa, idan wata ta fito waje ko da tsirara take yawo, tsanani mutum ya kawar da kai, ya nemi tsarin Allah. Kada ya ƙara kallo.

Duk da haka, malamin ya ce su ma mata akwai haƙƙi kansu na yin shigar kamala. Da kuma guje wa aikata duk abin da zai ja hankalin wani matuƙar yin hakan bai kamata ba.

A baya-bayan nan dai, al’ummar Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa saboda ƙaruwar ayyukan fyaɗen da ake samu a kan mata da ƙananan yara, lamarin da ya kai ga kiraye-kirayen a ƙara tsananta hukunci.

Lamarin da shi ma malamin ya nanata, inda yana da kyau a ƙarfafa dokoki a kan batun fyaɗe sannan a tabbatar ana aiki da su kan mutanen da kotu ta kama da laifi.

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Police force

Image caption

Mohammed Adamu ya ce zuwa yanzu an kama mutum 799 da ake zargi yayin da aka gudanar da bincike kan lamari 631 aka kuma gurfanar da su a kotu

Sheikh Pantami ya ce haƙiƙa akwai buƙatar sake waiwayar dokoki musamman saboda yadda matsalar fyaɗe ke neman zaman ruwan dare a Najeriya.

“Akwai abin da suke cewa lacuna a law shi ne sai ka ga wata magana ta yi harshen damo. Sai ka ga (ma’anarta) ba ta fito fili ba, sai a je kotu a yi ta musu,” in ji shi.

Ya ce ya dace a yi doka tsayayyiya, wadda za ta fayyace ƙarara cewa duk wanda ya yi abu kaza, hukuncinsa kaza ne.

Malamin addinin Musuluncin ya kuma buƙaci shigar da hukunce-hukuncen addini cikin dokokin yaƙi da fyaɗe, tun da a cewarsa addini ya yi magana a kansu.

“Idan fyaɗe babu aiki da ƙarfi, babu baarzana ga ran mace ko ga mutuncinta, to ana ɗaukar wannan al’amari a matsayin zina ne kamar yadda ya zo cikin suratul Annur,” in ji minista.

Sai dai ya ce matuƙar an yi amfani da ƙarfi da barazana kamar ta makami, to wannan hukuncinsa na cikin suratul Ma’idah.

Dr. Pantami ya kuma ce waɗannan dokoki ne Allah, kuma al’ummomin da suka kwatanta aiki da su, sun zauna lafiya.

Don haka ya buƙaci jihohin Najeriya su yi nazari kan dokokin da suke da su, kuma su dubi hanyoyin da za su ƙarfafa su, tare da tabbatar da aiki da dokoki ga masu aikata fyaɗe.

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...