Bayern Munich 4-0 Wolfsburg: Robert Lewandowski ya haura Gerd Muller a cin kwallaye a Bundesliga a shekara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Lewandowski ya ci kwallo 69 a wasa 59 a Bayern Munich da kuma tawagar Poland a 2021

Robert Lewandowski ya ci kwallo na 43 a Bayern Munich a shekarar 2021, ya kuma haura tarihin Gerd Muller a cin kwallaye a Bundesliga a shekara daya.

Dan wasan tawagar Poland, mai shekara 33, shine ya ci na hudu saura minti uku a tashi a karawar da Bayern Munich ta casa Wolfsburg 4-0 a Allianz Arena a gasar Bundesliga.

Gerd Muller ya kafa tarihin cin kwallo 42 a gasar Bundesliga a shekarar 1972, tun daga lokacin ba wanda ya ci yawan kwallayen a shekara daya sai a wannan lokacin.

Nasarar da Bayern ta yi ya sa ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki tara tsakaninta da Borussia Dortmund.

A watan Mayu, Lewandowski ya haura tarihin tsohon dan kwallon Bayern Munich, Muller mai shekara 49 da cin kwallo 41 a kakar 2020-21.

Thomas Muller, wanda ya buga wasa na 400 a babbar gasar Jamus ne ya fara cin kwallo a minti na bakwai da taka leda daga baya Dayot Upamecano ya kara na biyu.

Leroy Sane ne ya kara na uku, sannan Lewandowski ya ci na hudu.

More from this stream

Recomended