Bayanai na kara fitowa kan harin Burkina Faso | BBC News

Burkina Faso na fuskantar hare-haren ta'addanci sosai daga kungiyoyi
Image caption

Burkina Faso na fuskantar hare-haren ta’addanci sosai daga kungiyoyi

Bayanai na kara fitowa kan harin da ‘yan bindiga suka kai a Burkina Faso da ya kashe gwamman fararen hula yayin da ake zaman makoki na kwana biyu.

Bayanan da jami’an tsaro suka tabbatar na nuna cewa sama da mahara 200 a kan babura suka kai tagwayen hare-haren dauke da manyan makamai.

To amma kafin sojojin da ke sintiri a yankin su iya tunkararsu tuni sun hallaka jama’a da dama a wani shingen binciken soji da ke yankin Soum.

A Soum din kawai ‘yan tada zaune tsayen sun hallaka mutun 35 kusan dukkansu mata, tare da wasu sojoji bakwai.

To sai dai bayan wani kukan-kura ne jami’an tsaron suka samu nasarar kashe ‘yan bindigar tamanin, a cewar gwamnati.

A cewar ministan tsaron Burkina Faso Cherif Sy, kasar na neman hadin kan al’umma a yankin matsawar ana son shawo kan ta’addanci a yankin.

Burkina Faso ta zamo kasa a nahiyar Afrika ta baya bayan nan da ke fuskantar haren haren yan bindiga da ke da nasaba da tsatstsauran ra’ayin addini daga wasu kungiyoyi.

Masana na ganin cewa hare-haren ta’addanci na karuwa ne a yammacin Afrika saboda rashin samar da isasshen tsaro daga kasashen.

Ko a ‘yan makonnin da suka gabata ‘yan bindiga sun hallaka sojojin Nijer 71 a wani hari kan iyakarta da Mali.

A yanzu gwamnati a Ouagadougou ta ayyana zaman makoki na kwana biyu, yayin da ake ci gaba da zaman zullumi a kasar.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...