
Bayan tirka-tirka da tashin-tashina da aka asha a karshe dai Kabiru Tanimu Turaki zaɓaɓɓen shugaban jam’iyar PDP ya shiga ofishinsa dake hedkwatar jam’iyar a ginin Wadata Plaza a birnin tarayya Abuja.
Hedkwatar jam’iyar ta PDP ta kasance a cikin rudani a yayin da tsagin jam’iyar da basa ga maciji da juna ke ƙoƙarin ganin sun kwace iko da ginin hedkwatar jam’iyar.
Da yake magana da yan jaridu a ranar Litinin Turaki ya zargi tsagin jam’iyar dake samun goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike da hayar yan daba domin tayar da zaune tsaye a hedkwatar jam’iyar ta yadda gudanar da taron shugabannin da aka zaba zai gagara.
“Sun zo nan da yan daba dauke da makamai kamar yadda muka yi tsammani za su hargitsa mana taro amma cikin ikon Allah mun samu nasarar maganinsu,” ya ce
Turaki ya ce a karshe sun samu karbe iko da ginin sakatariyar jam’iyar bayan kokarin da aka yi na hanasu.
Sabon shugaban ya yi allahwadai da rawar da Wike ya ke takawa a rikicin jam’iyar ta PDP.

