
Yan sanda a jihar Ogun, suna tsare da wata uwa mai shekaru 33 wacce ake zargin ta da sayar da ƴarta mai watanni 18 kan kuɗi N600,000 domin ta biya bashin banki da ta ci.
Mutumin da ya saya wanda yanzu haka ya cika wandonsa da iska an ce ya sayi yarinyar ne a jihar Lagos.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ogun ya fadawa yan jaridu a Abeokuta ranar Litinin cewa an kama matar ne biyo bayan korafi da mijinta,Nureni Razaq ya shigar a ofishin yan sanda dake Sango.
Mai magana da yawun rundunar ya ce a cewar mijin matar ta tafi Lagos tare da yarsu mai suna Moridiat Razaq amma kuma ta dawo gida ba tare da yarinyar ba.
Bayan yin duk kokarin da ya kamata domin jin abun da ya faru ga yarinyar ya ci tura mijin ya mika batun ga ofishin yan sanda.
DPO din yan sanda na Sango, Dahiru Saleh ya bada umarnin gaggawa ga yan sanda masu bincike da su kama matar.
A yayin binciken ne matar ta bayyana cewa ta sayar da yarinyar kan kuɗi naira dubu ɗari shida a Lagos.