Barcelona za ta karbi bakunci Atletico Madrid a makon fidda gwani

Getty

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a makon fidda gwani, yayin da Real Madrid za ta fafata da Sevilla.

Duk da cewa Atletico ta ba da maki 13 a watan Janairu, amma idan Barcelona da ke matsayi na uku ta samu nasara a wasan za ta iya komawa ta daya a gasar a karon farko.

Real dake ta biyu da maki iri daya da Barcelona za ta fafata da Sevilla da ke matsayi na hudu a ranar Lahadi.

Kungiyar ta Zinedine Zidane na da damar darewa kan teburi sama da Barcelona da Atletico saboda ka’idar wanda ya ci wani a gasar a gida da waje.

‘Ba wani mamaki a matsayin da muke a yanzu’

Kocin Barcelona Roland Koeman wanda ba zai fito a matsayin koci ba a wasan saboda korarsa da aka yi a wasan baya kan maganganun da ya fada wa alkalin wasa, wanda da farko ba a yi zato za su kawo wannan matsayi ba.

Kungiyar bangaren Cataloniyan sun koma cikin tseren cin gasar ne bayan nasarar da suka samu a wasa 16 cikin 19 a wannan shekara, a yanzu kuma suna na uku da maki biyu tsakaninsu da Atletico yayin da ya rage wasa hudu kacal a gasar.

“Bani da tabbas ko sakamakon wannan wasan zai zama hukuncin karshe amma abin da na yi amanna da shi, shi ne wasan na da mahimmanci” in ji Koeman.

“Muna karawa ne da kungiya biyu domin samun nasarar cin wannan gasa, Ba wani mamaki a matsayin da muke a yanzu saura watanni kadan. Mu zama zakaru, muna da mukatar cin ko wanne wasa.

More from this stream

Recomended