Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Barcelona ta yi nasarar durawa Real Betis kwallo 5-2 a wasan mako na biyu a gasar cin kofin La Liga da suka fafata ranar Lahadi a Camp Nou.
Barcelona ta ci kwallayen ne ta hannun Carles Perez da Jordi Alba da Arturo Vidal da Antoine Griezmann wanda ya ci biyu a fafatawar.
Real Betis ta ci nata kwallayen ne ta hannun Nabil Fekir da kuma Loren Moron.
Sakamakon wasannin La Liga mako na biyu da aka kara ranar Lahadi:
- Deportivo Alaves 0 – 0 RCD Espanyol
- Real Mallorca 0 – 1 Real Sociedad
- Leganes 0 – 1 Atletico de Madrid
Ranar Asabar ce Barcelona za ta ziyarci Osasuna a wasan mako na uku a gasar ta La Liga, a ranar ita kuwa Real Betis za ta karbi bakuncin Leganes.
A wasan makon farko da aka fara La Liga ta bana wato 16 ga watan Agusta, Barcelona rashin nasara ta yi da ci 1-0 a gidan Athletico Bilbao.