Barcelona na son Eric Garcia, Chelsea ta kusa ɗauko Havertz

ERIC

Barcelona tana son dauko dan wasan Manchester City mai shekara 19 dan kasar Sufaniya Eric Garcia a bazarar da muke ciki. (Goal.com)

Chelsea na dab da amincewa da yarjejeniya da Bayer Leverkusen don dauko dan wasan Jamus mai shekara 21 Kai Havertz. (Teamtalk)

Dan wasanArsenal Pierre-Emerick Aubameyang yana duba yiwuwar tafiya Chelsea a watan Janairu sai dai the Blues ba za ta iya biyan dan wasan mai shekara 31 babban alawus-alawus da yake so a ba biya shi ba. (Mailonline)

Everton ta ware £18m don dauko da wasan Real Madrid mai shekara 23 dan kasar Sufaniya Sergio Reguilon. (Sky Sports)

Ole Gunnar Solskjaer yana son Manchester United ta kara kaimi a yunkurinta na dauko dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, domin kaucewa abin da ya faru a kakar wasan da ta wuce inda suka gaza dauko Harry Maguire. (ESPN)

Borussia Dortmund za ta yi yunkurin dauko dan wasan Netherlands kuma tsohon dan wasan Manchester United Memphis Depay, mai shekara 26, daga Lyon idan United ta dauko Sancho. (Bild – in German)

Za a bayar da dan wasan Barcelona Philippe Coutinho, mai shekara 28, ga Arsenal da Tottenham Hotspur, kuma akwai dama guda daya wacce za ta sa Gunners ta dauko dan wasan na Brazil inda za ta biya Barca £9m da kuma dan wasan Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 21. (Independent)

Real Betis na sha’awar dauko dan wasan da Arsenal take zawarci Dani Ceballos. Dan wasan na Sufaniya mai shekara 23 yana zaman aro a Arsenal daga Real Madrid. (Onda Cero, via Sun)

Barcelona da kungiyar David Beckham Inter Miami sun nemi dauko dan wasan Chelsea dan kasar Brazil Willian, 31. (Sky Sports)

Dan wasan Bournemouth Callum Wilson, mai shekara 28, ya gaya wa abokansa na kungiyar cewa yana son barin kungiyar. (Telegraph)

Tottenham ba za ta sayar da dan wasan Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 23 ba, duk da sha’awar dauko da Inter Milan take yi.(PA, via the42)

Fulham, Bournemouth da kumaStoke City suna son dauko dan wasan Ingila mai shekara 21 Mallik Wilks, wanda a watan jiya Hull City ta saye shi. (Football Insider)

Dan wasan Ingila Jeremy Ngakia, mai shekara 19, yana dab da tafiya Watford bayan ya bar West Ham. (Guardian)

More News

An ji ƙarar harbe-harbe a fadar Sarkin Kano

A daren ranar litinin ne aka bayar da rahoton jin harbin bindiga a kusa da karamar fadar inda hambararren Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero,...

Ministan shari’a nason INEC ta riƙa shirya zaɓen ƙananan hukumomi

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya yi kira da a soke hukumar zaɓen jihohi masu zaman kansu. Da yake magana a...

Kotu ta hana Aminu Ado ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

Babbar Kotun jihar Kano ta hana Aminu Ado Bayero ayyana kansa a  matsayin Sarkin Kano har sai ta kammala sauraron ƙarar dake gabanta. Kotun ta...

NDLEA ta kama wani ɗan kasuwa da ya haɗiye ƙunshi 111 na hodar ibilis  a filin jirgin saman Abuja

Jami'an Hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi  sun kama wani mutum mai suna Emmanuel Orjinze wani ɗan kasuwa akan...