
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Barcelona ta sanar ranar Litinin cewar ta sasanta da Neymar kan takaddamar da ke tsakaninta da wasan tawagar Brazil.
Dan kwallon Brazil da Barcelona sun samu takaddama a tsakaninsu, bayan da Barcelona ta sayar da Neymar ga Paris St-Germain a 2017.
Neymar ya yi zargin Barcelona ba ta biya shi alawus a kwantiragin da ya saka hannu a Oktobar 2016, kafin ya koma Paris St Germain kan Yuro miliyan 222 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya.
Hakan ne ya sa dan wasan Brazil ya kai Barcelona kara domin a biya shi Yuro miliyan 46.3, ita kuma kungiyar Barcelona ta yi karar shi da cewar ya karya ka’idar yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
Wani alkali a Barcelona ya yanke hukuncin a cikin watan Yuni cewar Neymar ya biya kungiyar Camp Nou Yuro miliyan 6.7.
Wasu kafar yada labarai a Sifaniya sun ce Neymar ya daukaka kara ya kuma kara maka Barcelona a kotu kan wani zargin na da ban.
Barcelona ta sanar da cewar ta yi sulhu da Neymar, an kuma kawo karshen tuhume- tuhumen da ke tsakaninsu a kotu yanzu komai ya wuce.