Bani da niyar takarar shugaban kasa a 2023- Buratai

Tsohon babban hafsan sojan kasa na Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya nesanta kansa daga wasu fastocin takarar shugaban kasa dake yawo a gari.

Buratai wanda yanzu haka shi ne jakadan Najeriya a jamhuriyar Benin, Ya ce bai taba nuna sha’awarsa, tattaunawa ko kuma bawa wani umarni kan batun.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da tsohon mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Sani Usman ya fitar.

Sanarwar ta shawarci al’umma da suyi watsi da fastocin domin ba daga wurin sa suka fito ba.

More News

Jihar Neja Ta Yi Rajistar Mutane 289 Da Suka Kamu Da Cutar Amai Da Gudawa, 17 Sun Mutu

Wata annobar cutar amai da gudawa a Jihar Neja ta yi sanadin mutuwar mutane 17 tare da kama mutane 289 a kananan hukumomi 11...

An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers. Ƙona ginin na zuwa...

Ƴanbindiga sun hallaka wani shugaban APC a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Bako Bala, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, a yayin wani yunkurin yin garkuwa da...

Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka...