
Siminalayi Fubara dakataccen gwamnan jihar Ribas ya ce bashi da wata alaƙa da wata ƙungiya ta masu tayar da kayar baya a yankin Neja Delta.
Akwai dai zargin da ake yi cewa gwamna Fubara na da alaƙa da wasu masu tayar da ƙayar baya da ke da hannu akai hare-hare kan bututun mai da kuma wasu wuraren hakar mai a jihar ta Ribas.
A wata sanarwa ranar Litinin, Nelson Chukwudi mai magana da yawun gwamnan ya ce Fubara ba zai goyi bayan kowane irin nau’i na ayyukan batagari ba a jihar Ribas ko kuma yankin Neja Delta baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa waɗansu ne suka kirƙiri fefan bidiyo na ƙarya suna alaƙanta gwamnan da ƴan tayar ƙayar bayan.
Gwamnan ya bukaci jami’an tsaro da su binciki inda bidiyon ya fito kana su ɗauki a mataki akan waɗanda ke da hannu akai.