Ban taba yin fim kamar Mansoor ba — Ali Nuhu

[ad_1]

Umar M Sharif da Maryam Yahaya

Hakkin mallakar hoto
Yotube

Image caption

Umar M Sharif da Maryam Yahaya ne jaruman Mansoor

Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya ce bai taba shirya fim din da ya yi amfani da fasahar kirkire-kirkire a kansa kamar Mansoor ba.

Mansoor ya lashe lambar yabo ta fim mafi kayatarwa da aka shirya a cikin Najeriya [rukunin Hausa] a bikin Africa Magic Viewers Choice Awards na bana, wanda aka yi a birnin Lagos ranar Asabar da daddare.

Fim ɗin Mansoor, wanda jarumin ne ya shirya kuma ya ba da umarni, labari ne na wani matashi ɗan gaba-da-fatiha.

Mahaifiyar Mansoor ta yi ƙoƙarin ɓoye masa wani sirri game da asalinsa, sai dai soyayya ta sanya shi neman sanin gaskiyar al’amari.

Iyayen wata yarinyar da soyayya ta hada su a sakandare ne suka yi masa gorin asali, inda hakan ya tilasta masa katse karatu, ya bazama duniya don gano mahaifinsa.

‘Abin da ya sa muka lashe gasar’

Ali Nuhu ya shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ya yi matukar jin dadi da fim din ya yi zarra cikin sauran fina-finai.

A cewar sa, “Ina ganin Mansoor ya samu wannan nasara ce saboda bamu taba shirya fim wanda aka yi amfani da fasahar kirkire-kirkire kamar sa ba; mun kashe kudi sosai sannan mun yi amfani da na’urori na zamani wurin daukar fim din.”

Jarumin na Kannywood ya kara da cewa yanzu bai san adadin lambobin yabo da kyautukan da ya samu ba a harkar yin fina-finai, yana mai shan alwashin ci gaba da shirya fina-finai masu kayatarwa.

‘Juriya da tawakkali’

Ali Nuhu ya ce jigon Mansoor shi ne juriya da tawakkali don samun waraka ga wani halin alhini da ɗan adam ka iya fuskanta a rayuwa.

“Akwai soyayya a cikinsa, amma jigonsa ba soyayya ba ce. Darasin da yake ƙoƙarin isar wa al’umma shi ne duk abin da ka ga ya samu mutum a rayuwa…kar ka yi masa gori.”

Ya ci gaba da cewa “kar ka tsangwame shi a kan wannan abu domin mai yiwuwa hanyar da Allah Ya jarabce shi ke nan, kamar yadda kai ma a matsayinka na ɗan Adam akwai hanyar da Allah Ya jarabce ka.”

Saɓanin yadda aka saba ganin fitattun jarumai a fina-finan Kannywood, a fim din Mansoor an yi amfani da wasu sabbin fuskoki a matsayin manyan jarumai, da suka haɗar da Umar M Sharif da Maryam Yahaya.

Sama da shekara 20 ke nan da fara harkar fina-finan Hausa (Kannywood), amma masu sharhi na sukar cewa ba a sanya fasahar zamani sosai a cikin fina-finan.

Sai dai masu fim ɗin Mansoor sun ce sun yi ƙoƙarin tunkarar wannan ƙalubale wajen haɗa shi, don haka ne ma a cewarsu, fim ɗin ya kasance mafi tsada a duniyar Kannywood, don kuwa an kashe kusan naira miliyan takwas wajen hadawa da tallata shi.



[ad_2]

More News

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...