Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Jami’an tsaro sun killace inda aka kai harin don fara gudanar da bincike
Wani jami’in dan sanda ya rasa ransa yayin da wadansu mutane suka ji mummunan rauni bayan wani harin kunar bakin wake a babban birnin kasar Tunusiya, wato Tunis a ranar Alhamis.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam din da ke jikinsa a gaban wata motar ‘yan sanda a kan titin Charles de Gaulle a kusa da ofishin jakadancin Faransa.
‘Yan sanda biyu da fararen hula biyu ne suka ji raunuka, kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta bayyana.
Mahari na biyu ya tada bam din da ke jikinsa ne jim kadan bayan na farkon a kusa da wani ofishin ‘yan sanda da ke yankin al-Qarjani, a cewar ma’aikatar. Mutum hudu ne suka jikkata sanadiyyar wannan harin.
Sai dai kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Hakazalika an taba samu irin wannan harin a kan wata babbar hanya a birnin, mai suna Avenue Habib Bourguiba, a bara inda mutum tara suka yi raunuka.
An kuma taba samun wani hari a wani gidan adana kayan tarihi a birnin Tunis, inda mutum 22 suka mutu. Kodayake ‘yan kungiyar IS ne suka dauki alhakin kai harin a lokacin.