Kwararru a fannin noma sun ba da shawarar cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya nada kwararren masani a matsayin ministan noma maimakon dan siyasa.
A yayin tattaunawa da ƴan jarida, sun bayyana muhimman batutuwan da ke bukatar kulawa daga gwamnatin Najeriya mai zuwa a fannin noma tare da jaddada karfinta na samar da karin kudin shiga ga al’ummar kasar.
“Na farko dai babu wani yanayi da za a sanya dan siyasa a matsayin ministan noma, na biyu kuma dole ne sabuwar gwamnati ta gane cewa noma kasuwanci ne,” in ji kodinetan kungiyar kasuwanci ta Najeriya Agri-Business, Emmanuel ljewere.
ljewere ya bayyana kowane manomi a matsayin dan jari hujja, yana mai jaddada cewa manoma ba ma’aikatan gwamnati ba ne.