
Gwamnan jihar Niger, Umar Bago ya bayar da umarnin gaggauta sake bude jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) dake garin Lapai a jihar.
A ranar 25 ga watan Yuni ne Bago ya bayar da umarnin rufe jami’ar saboda damuwa kan barazanar tsaro.
A wancan lokacin gwamnan ya ce an dauki matakin ne saboda tarbarbarewar tsaro a cikin jami’ar.
Gabanin rufe makarantar dalibai sun gudanar da zanga-zanga kisan da aka yi wa abokin karatunsu a lokacin da aka yi wani fashi da makami a jami’ar.
A wata sanarwa ranar Juma’a, Lawan Tanko jami’in yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin jihar ya ce Bago ya bayar da umarnin a cigaba da karatu a jami’ar tun daga ranar 04 ga watan Agusta.
Tanko ya ce Bago ya shawarci dukkanin daliban da za su dawo da kuma ma’aikata su bi tsarin tsaro sau da kafa kana su bada hadin kai ga hukumomin jami’ar.