Bafarawa Ya Musanta Shirin Komawa APC a Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, Muhammadu Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa ba shi da niyyar komawa jam’iyyar APC mai mulkin ƙasa, yana mai jaddada cewa ya riga ya yi ritaya daga harkokin siyasa.

Da yake magana da manema labarai, Bafarawa ya ce tun da dadewa ya bayyana ficewarsa daga siyasa, ko ta hanyar zaɓe ko ta naɗi.

A cewarsa, batun shiga kowace jam’iyya bai taso ba. Ya ce, “Idan za a iya tunawa na ce na bar siyasa ko ta zabe ko ta nadi, kuma babu wata jam’iyya da zan shiga, amma zan shiga kungiyar taimakawa matasa da sauransu.”

Bafarawa ya yi wannan bayani ne bayan da dubban magoya bayansa suka koma jam’iyyar APC a jihar Sokoto, lamarin da suka alakanta da gamsuwarsu da yadda gwamnan jihar, Ahmad Aliyu, ke tafiyar da mulki.

More from this stream

Recomended