Wani sabon rahoto da cibiyar nazarin dimukurdiyya da ci gaban kasa ta CDD ta fitar ya bankado yadda shugabanin sojojin Najeriya suka yi dumu dumu a harkar cin hanci na kudade har dala bilyan 15 a cikin shekaru 20
Rahoton tonon sililin da binciken kwakwaf da kungiyar bunkasa dimukurdiyya da ci gaban kasa ta CDD ta fitar mai shafuka 27 ya tabo batutuwa da dama a shekaru 20 na yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya Inda ya bankado yadda ta hanyar bada kwangiloli na boge shugabanin sojojin Najeriyar suka salwantara da dala bilyan 15 na kudaden da aka ware domin samar da tsaro. Auwal Musa Rafsanjani na kungiyar Cislac mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya ce rahoton bai basu mamaki ba.
An dai yi zargin amfani da ‘yan boko wajen mayar da harkar tsaron Najeriya zama tamkar wata haja da ake kasuwanci da ita, abinda ya haifar da lalacewar al’amurran da ma karuwar mutanen da ke rasa muhallansu a dalilai na rashin tsaro. Rahoton da ya duba sassa daban daban na matsalar cin hanci da rashawa a Najeriyar ya tunato da irin abinda gwamnatin da kanta ta bankado a lokacin da ta karbi mulki na badakar makamai.
Duk da bankadowar kungiyar ta CDD ta yaba wa gwamnatin Najeriyar a fanin kafa dokoki na yakar cin hanci da rashawa tare ma da samar da hukumomi irin EFCC da ICPC da ta ikon bada bayanai a kan aiyyukan gwamnati.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar tsaron Najeriya Brigadier General Onyema Nwachukwu ya ci tura. Amma ministan yada labarun kasar Lai Mohammed ya sha nanata irin kokarin da Najeriyar ke yi.
Najeriya dai ta yi kaurin suna a kan matsalar cin hanci da rashawa da kudadden da aka sace daga kasar ta wannan mumunar dabi’a da ya zarta misali da ma lissafi.