Babu sansanin sojan kasashen waje a Najeriya -Ribadu

Mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce babu sansanin sojojin ƙasashen waje a Najeriya.

Ribadu ya bayyana haka a matsayin martani kan zargin da shugaban mulkin soja na ƙasar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya yi na cewa Najeriya na haɗa kai da ƙasar Faransa domin kawo ruɗani a ƙasar Nijar.

An daɗe dai ana zaman doya da manja a tsakanin ƙasashen biyu tun bayan da Tchiani ya jagoranci hamɓarar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Nijar, Bazoum Mohammed.

Da yake magana da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ma shawarcin shugaban ƙasar ya ce iƙirarin da shugaban Nijar ya yi ƙarya ce tsagoranta.

Ribadu ya ce kamata ya yi Nijar da Najeriya su haɗa ƙarfi domin su yaƙi Lakurawa da suka haifar da matsalar tsaro a duka ƙasashen biyu..

“Babu tantama shugaban Nijar ya san Najeriya ciki da bai amma ina so ku ƴan jaridu kuje wuraren da ya ambata ku gani da idonku ko kuma ku tambayi mazauna yankin ko akwai ɗan ƙasar waje ballantana  sojoji daga wata ƙasar,” ya ce.

“Ya kamata shugabannin mulkin sojan Nijar su sani cewa mu Najeriya ba matsala ce a gare su ba,” ya ce.

“Waɗannan ƴan ta’addar da muke yaƙa  matsalar mu ce baki ɗaya. Yakamata mu fuskance ta tare,”

Ribadu ya ce Najeriya za ta cigaba da aiki tare da Nijar saboda mutanen ƙasashen biyu ƴan uwan juna ne.

More from this stream

Recomended